Ka ji abin da aka yi wa Magu bayan Majalisa ta ki tabbatar da shi

Ka ji abin da aka yi wa Magu bayan Majalisa ta ki tabbatar da shi

Ibrahim Magu na EFCC ya karbi kyautar lambar yabo daga Jaridar Leadership a matsayin gwarzon bana bayan Majalisa ta ki amincewa da shi a matsayin shugaban EFCC

Ka ji abin da aka yi wa Magu bayan Majalisa ta ki tabbatar da shi

Ka ji abin da aka yi wa Magu bayan Majalisa ta ki tabbatar da shi

Jaridar Leadership ta karrama Ibrahim Magu na EFCC a matsayin gwarzon ta na shekara inda ya kuma sadaukar da kyautar ga mutanen Najeriya. Ibrahim Magu ya yaba da kokarin jama’ar kasar da suka mara masa baya wajen yaki da sata a kasar.

An dai duba mutane da dama wajen bada kyautar a fannin kasuwanci, waka, aikin gwamnati da kuma ilmi inda aka zabi Ibrahim Magu a matsayin wanda yayi zarra wannan shekara. Magu dai ya tinkari sata a kasar nan na dogon lokaci duk da cewa ba a tantance sa ba a Majalisa.

KU KARANTA: ASUU na shirin shiga wani yajin aiki

Hakan ma dai ta sa aka zabi Ibrahim Magu a cikin wadanda za su yi magana a wani taron kasa da kasa game da cin hanci da rashawa a Landan wannan makon. Magu dai zai yi magana ne a kan taken: a maido mana kudin mu.

Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki yayi magana game da batun rashin tabbatar da Ibrahim Magu na EFCC. Saraki yace Magu bai samu sa’a bane wajen tambayoyin da aka yi masa kamar yadda wasu kuma suka tsallake a baya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel