Saraki yayi magana game da Magu da Hamid Ali

Saraki yayi magana game da Magu da Hamid Ali

Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki yayi magana game da batun rashin tantance Ibrahim Magu na EFCC da kuma abin da ke faruwa tsakanin Majalisa da Hamid Ali na kwastam

Saraki yayi magana game da Magu da Hamid Ali

Saraki yayi magana game da Magu da Hamid Ali

Bukola Saraki ya bayyanawa wani gidan talabiji na TV Continential cewa ba saboda rahoton da DSS ta bada Majalisa ta ki tabbatar da Ibrahim Magu ba. Saraki yace Magu bai samu sa’a bane wajen tambayoyin da aka yi masa kamar yadda wasu kuma suka tsallake a baya.

Saraki yace idan har aka turo wani dabam yana iya dacewa ya tsallake tambayoyin. Bukola Saraki yace wannan sha’ani ne na aiki amma mutane ke kokarin su saka siyasa a ciki. Shugaban majalisar yace tabbas an dauki matakin da ya fi dacewa.

KU KARANTA: Sanotocin da su ka ki amincewa da Magu

Game da sauran batutuwan Bukola Saraki yace su kan yi shawara kafin su yi aiki kamar yadda dokar kasa ta bada dama. Saraki yace wasu ne dai ba su son Damukaradiyya don haka suke ta babatu.

Bayan abin da ya faru ne Sanata Ali Ndume yace Bukola Saraki bai dace da shugabanci ba. Ndume yace idan har haka ake aiki to da Bukola Saraki bai dace ya zama shugaban Majalisar ba don kuwa ana zargin sa shi ma da wasu laifuffuka a Kotu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel