Mutane 7 sun mutu a harin kunar bakin wake da aka kai Maiduguri

Mutane 7 sun mutu a harin kunar bakin wake da aka kai Maiduguri

Mutane bakwai sun mutu a harin kunar bakin wake da aka kai a daren ranar Asabar a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Mutane 7 sun mutu a harin kunar bakin wake da aka kai Maiduguri

Mutane 7 sun mutu a harin kunar bakin wake da aka kai Maiduguri

Yan kunar bakin wake uku, da wasu hudu da suka hada da yara biyu ne suka mutu a harin. An kuma bayyana cewa mutane takwas ne suka ji raunuka sannan kuma an kai su asibiti.

A wani sanarwa daga jami’in kula da huldan jama’a na hukumar yan sandan jihar Borno, Victor Isuku, harin ya afku ne da misalin karfe 9 na daren ranar Asabar a wajen garin Maiduguri.

KU KARANTA KUMA: Wani dan Najeriya mai shekara 43 yayi kashin hodar iblis a filin jirgin sama na Lagas

Sanarwan ya zo kamar haka: “wasu yan kunar bakin wake uku, namiji daya da mata biyu, sunyi yunkurin tayar da garin Maiduguri ta kauyen Umarari a yankin Molai.

“Yan bangan JTF ne suka gano sannan suka kalubalance su. Sun tayar da bama-bamai dake jikinsu a lokacin da suka gudu zuwa shashi daban-daban.

“Mutane hudu wanda suka hada da dan bangan JTF, wata mata da kuma yaranta guda biyu yayinda wasu mutane takwas suka ji raunuka, sannan kuma aka dibe su zuwa asibiti.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel