Abun murna: Ma'aikata zasu dara, Buhari zai yi karin albashi

Abun murna: Ma'aikata zasu dara, Buhari zai yi karin albashi

- Gwamnatin tarayya za ta duba yiwuwar soma biyan Naira dubu 50 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata.

- Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Sanata Chris Ngige ya ce nan da dan wani lokaci shugaban kasa Muhammadu Buhari zai amince da kafa wani kwamiti mai wakilai 29 domin tattaunawa da kungiyoyin kwadago don fitar da tsarin mafi karancin albashin ma’aikata a kasar nan. An tsammanin mafi karancin albashin shine naira dubu hamsin.

Abun murna: Ma'aikata zasu dara, Buhari zai yi karin albashi

Abun murna: Ma'aikata zasu dara, Buhari zai yi karin albashi

Mista Ngige ya kuma ce rahoton da kwamitin sake fasalin mafi karancin albashi na kasa zai bayar za kuma a mika shi ga majalisun tarayya domin dubawa kafin aiwatar da shi.

A wani labarin kuma, Babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN) ya kara jaddadawa jama'ar kasa cewa tabbas darajar Naira fa zata kara yin sama a cikin satin nan mai kamawa.

Mai magana da yawun babban bankin Isaac Okorafor shine yayi wannan bayanin a cikin wata sanarwar da ya fitar ga manema labarai. Mr. Isaac ya kara da cewa hakan zai tabbata ne kuwa saboda babban bankin ya gama dukkan shirye-shirye don kara zuba daloli a bankunan kasar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel