Wani dan Najeriya mai shekara 43 yayi kashin hodar iblis a filin jirgin sama na Lagas

Wani dan Najeriya mai shekara 43 yayi kashin hodar iblis a filin jirgin sama na Lagas

An kama wani mutumi mai shekaru 43 sannan aka sanya shi kashin hodar iblis kulli 66 a filin jirgin Lagas, a hanyarsa ta dawowa daga kasar Kenya.

A cewar rahotanni, an kama wani mutumi mai shekaru 43 mai suna Anukaenyi Bob-Manuel Ogochukwu, a filin jirgin sama na Lagas dauke da hodar iblis a jikin sa.

Anukaeanyi wanda yayi ikirarin kasancewar sa malamin kwamfuta daga jihar Anambra, na a hanyarsa ta dawowa daga kasar Kenya lokacin da aka kama shi sannan kuma aka sanya shi kashin kullin muggan kwayoyi guda 66 dake jikin sa.

A cewar mai laifin, ya fara safaran miyagun kwayoyi ne saboda yana bukatar kudin da zai kula da dansa wanda ke fama da ciwon zuciya sannan kuma yake ganin likita a wani asibiti dake Nairobi.

KU KARANTA KUMA: Mahaifina na bani N500 a duk lokaci da ya kwana da ni – yar shekara 15 ta koka

Da yake tona asirin laifin sa, Anukaenyi wanda ke auran wata mutumiyar Kenya, yace:

“Ina koyawa a wani makarantar kwanfuta dake Onitsha, jihar Anambra. Wannan shine karo na farko da nake alaka da miyagun kwayoyi. Nayi safaran miyagun kwayoyi don na ceto dana dake rashin lafiya. Likita yace dana na da rami a zuciya. Naje gurin mutane da dama don neman taimako amma babu wandaa ke da niyan taimaka mun sai dai wani mai safaran miyagun kwayoyi.

Dana na cikin mawuyacin hali na rayuwa ko mutuwa a wani asibiti dake Nairobi. Mai dilan kwayoyin wanda ya fito daga Tanzania yayi alkawarin biyana $2,000 kudin maganin dana. Ina cikin damuwa game da halin da dana ke ciki”.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kungiyar Boko Haram, Shekau, ya fito a sabon bidiyo

Da yake magana kan al’amarin, shugaban hukumar NDLEA Muhammad Mustapha Abdallah, yace:

“Babu bayani da zai wanke wanda ya aikata laifi. Safaran miyagun kwayoyi laifin ta’addanci ne kuma za’a hukunta wanda ake zargi daidai da laifinsa. Abunda mai laifin yayi ya dada birkita halin da yake ciki ne saboda yana fuskantar cajin aikata laifi yayinda nauyin kula da dansa mara lafiya ya koma kan wuyan matarsa a yanzu.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel