El-Rufa’I na kokarin fadawa jama’a cewa yafi Buhari – Sanata Shehu Sani

El-Rufa’I na kokarin fadawa jama’a cewa yafi Buhari – Sanata Shehu Sani

Sanata Shehu Sani yace wasikar da Gwamna El Rufa’I ya aikawa Buhari wata irin usulubi ne na nunawa jama’a cewa zai iya maye gurbin Buhari a 2019

El-Rufa’I na kokarin fadawa jama’a cewa yafi Buhari – Sanata Shehu Sani

El-Rufa’I na kokarin fadawa jama’a cewa yafi Buhari – Sanata Shehu Sani

Sanata Shehu Sani wanda ke wakiltan Kaduna ta tsakiya ya tuhumci gwamnan jihar Kaduna na rashin biyayya ga shugaba Buhari.

Yace: “ Gwamnan nada ra’ayinsa amma akwai tanakudi cikin maganarsa: na daya shine yana tuhuma ta da rashin yi masa biyayya da shugaban kasa saboda na fadi ra’ayina, amma gashi nan shima yana cin mutuncin shugaban kasan da jam’iyya, sai ya wayance da cewa wasika ya rubuta ya bari yan jarida suka gani, wanda ke nuna cewa shine mara biyayya kuma mara kunya..

KU KARANTA: Shugaban Kastam Hamid Ali ya shigesu

" Na biyu, duk abinda yake tuhumar shugaban kasa da shi, na shi ma tafi baci, fari daga kusoshi a gwamnatinsa da kuma rashin iya mulki.

“Babbanci shine shi shugaban kasa nada hakuri idan an soke shi. Amma gwamnan yace ina sukarsa ne saboda ina son zama gwamnan jihar Kaduna, wanda ke nuna cewa shima wannan wasika da ya rubuta wani usulubi na nuna cewa yafi Baba iyawa.”

"Wadanda suka san tarihi na sun sani cewa banida boye-boye, fitowa nike inyi magana yadda yake.”

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel