WAEC ta kawo sabon tsari

WAEC ta kawo sabon tsari

– Hukumar WAEC mai gudanar da jarrabawar kammala makaratar Sakandare ta kawo sabon tsari

– Yanzu za a fara gama aikin jarrabawar a cikin watanni 2

– Jama’a za su fara ganin sakamakon jarrabawar su da wuri

WAEC ta kawo sabon tsari

WAEC ta kawo sabon tsari

Hukumar WAEC mai shirya jarrabawar kammala karatun sakandare na kasashe yammacin Afrika ta kawo sabon shiri da sai sa wadanda suka rubuta jarrabawar su daina dadewa wajen jiran sakamako.

WAEC na kokarin ganin an kammala gyara jarrabawar sannan kuma a saki sakamako cikin kwanaki 60 rak. Shugaban Hukumar na Ofishin Najeriya ya bayyana haka a wani bikin kafuwar Hukumar da aka yi a Garin Legas.

KU KARANTA: Bankin Duniya ya ba Najeriya shaida

WAEC dai kan yi kwanaki 90 watau watanni uku cur kafin ta fitar da sakamakon jarrabawar, sai dai wannan karo ana kokarin a rage wannan lokaci kamar yadda Jaridar Premium Times ta bayyana.

Haka ma dai Hukumar JAMB ta rage lokacin da ake dauka wajen yin rajista domin rubuta jarrabawar ta shiga Makarantun gaba da Sakandare a kasar. JAMB tace daga yanzu wata guda kurum za a bada domin yin rajista Inji Shugaban Hukumar jarrabawar Farfesa Oloyede

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel