Najeriya ta fara fita daga matsalar tattalin arziki-Inji Bankin Duniya

Najeriya ta fara fita daga matsalar tattalin arziki-Inji Bankin Duniya

– Najeriya na fama da durkushewar tattalin arziki tun bara

– Babban Bankin Duniya yace ba za a dade Najeriya za ta mike ba

– Alkaluma sun bayyana cewa Najeriya ta kama hanyar farfadowa

Najeriya ta fara fita daga matsalar tattalin arziki-Inji Bankin Duniya

Najeriya ta fara fita daga matsalar tattalin arziki-Inji Bankin Duniya

Sanin kowa ne cewa a halin yanzu dai Najeriya na cikin matsi na tattalin arziki sai dai yanzu abubuwa sun fara farfadowa. Dama can mun yi bayani a wani rahoto inda muka bayyana cewa alkaluman na kyau ba tabarbarewa su ke yi ba.

Wata Jami’ar Babban Bankin Duniya ta bayyana cewa Najeriya ta kama hanyar fita daga matsalar tattalin arziki. Misis Eme Essien-Lore ta Bankin Duniya ta bayyana haka a karshen wannan makon.

KU KARANTA: Wani Gwamna ya koma Makaranta

Babban Bankin Duniya ya bayyana cewa rahotanni daga kungiyar lamuni na Duniya watau IMF sun bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya na motsawa gaba. Bankin Duniyar ya kira Gwamnati ta hada kai da masu hannun jari domin samawa Jama’a aiki.

An dai fara samun sauki wajen hauhawar farashin kaya wanda a da can dai kullum cikin tashi suke. Haka kuma jiimilar kudin kasar watau GDP yana ta kara yawa ne kamar yadda nazari ya nuna, sannan kuma darajar Naira na ta kara yawa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel