Dan wasa ya koma gatsar ayaba ana kwallo

Dan wasa ya koma gatsar ayaba ana kwallo

– Dan wasa Marcos Rojo ya ci ayaba ana cikin wasa

– Koci Mourinho yace Rojo ya ji yunwa ne ana wasa

– Kungiyar Man Utd ta karasa zagaye na gaba a Gasar UEFA Cup

Dan wasa ya koma gatsar ayaba ana kwallo

Dan wasa ya koma gatsar ayaba ana kwallo

Dan wasan bayan Kungiyar Man Utd Marcos Rojo ya tsaya cin ayaba yayin da ake wani wasa tsakanin Kungiyar ta Man Utd da Rostov na Gasar UEFA Europa League. Mourinho yace ba wani abin ban dariya bane don Dan wasan na sa ya ci ayaba.

Dan wasa Marcus Rojo dai ya gaji ne ana cikin wasan inda yayi tubus hakan ta sa ya nemi a miko masa ayaba. Wani Dan wasa ne ya mikowa Rojo ayaban ya kuma shiga gartsa abin sa. Man Utd dai tayi nasara a wasan ta kuma karasa zagaye na gaba.

KU KARANTA: Ana nema a saki kayan da aka kwace a Najeriya

Dan wasa ya koma gatsar ayaba ana kwallo

Dan wasa ya koma gatsar ayaba ana kwallo

Jose Mourinho ya koka bayan wasan inda yace wasanni sun masa yawa don kuwa zai kara kusan sau biyar a cikin kwanaki 10. Jose Mourinho yace hakan ba zai zo ga Kungiyar sa ta Man Utd da sauki ba.

Kwanaki zakaran Duniya Cristiano Ronaldo ya kafa tarihi a Duniya inda ya zama Dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a raga da kai. Haka kuma Ronaldo ne Dan wasan da ya fi kowa kwallaye a gidan Madrid watau filin Santiago Bernabeau.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel