Majalisan dattawa ta aika wasika ga fadar shugaban kasa

Majalisan dattawa ta aika wasika ga fadar shugaban kasa

Da kwai alamun cewa a ranan Juma’a 17 ga watan Maris, fadar shugaban kasa ta samu sako daga hannun majalisan dattawa akan kin tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaba hukumar hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC.

Ibrahim Magu : Majalisan dattawa ta aika wasika ga fadar shugaban kasa

Ibrahim Magu : Majalisan dattawa ta aika wasika ga fadar shugaban kasa

Kuma an tattaro cewa da alamun shugaba Muhammadu Buhari zai sake aika sunan Magu majalisan dattawan bisa ga shawaran ma’aikatansa musamman, shugaban kwamitin shawara akan yaki da rashawam Farfesa Itse Sagay.

A ranan Laraba 15 ga watan Maris, majalisan dattawa ta ki tabbatar da Ibrahim Magu saboda wata rahoton da hukumar DSS ta gabatar akanshi.

KU KARANTA: An damke masu garkuwa da mutane 3 a Kaduna

Amma fadar shugaban kasa ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana a ranan Alhamis cewa shugaban kasa ba zaiyi magana akan wannan al’amari ba har sai ya samu wasika daga majalisan dattawa.

Majiya ta bayyana cewa an baiwa shugaba Buhari shawaran sake gabatar da sunan Magu domin kada duniya ta ga cewa yayi kasa a guiwa wajen yaki da rashawa.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel