Gwamna El-Rufa’i ya koma Makaranta

Gwamna El-Rufa’i ya koma Makaranta

– Gwamnan Jihar Kaduna El-Rufa’i ya koma Makaranta

– Malam El-Rufa’i yana nema yayi digir-digir

– Gwamnan yayi watsi da rade-radin Jama’a

Gwamna El-Rufa’i ya koma Makaranta

Gwamna El-Rufa’i ya koma Makaranta

Jama’a dai suna ta yada rade-radin cewa an wuce da Gwaman Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i Turai zuwa asibiti a sakamakon rashin lafiya da ke damun sa. Wasu kuma su kayi ta yada cewa ana shirin tsige Gwamnan.

Wata Jami’a dai ta bayyana cewa Malam Nasir El-Rufa’i na cikin daliban da suka dauka domin yin karatun Digiri na uku. Gwamna El-Rufai’i zai yi digir-digir ne a fannin nazarin mulki a wata Jami’ar Majalisar dinkin Duniya da ke Kasar Holland.

KU KARANTA: Fayose yayi kaca-kaca da Obasanjo

Gwamna El-Rufa’i ya koma Makaranta

Gwamna El-Rufa’i ya koma Makaranta

Daya daga cikin Malaman Gwamnan Dr. Joe Abbah ya bayyana haka inda yake cewa ya kagara ya fara koyar da Gwamna El-Rufa’i a aji. Wannan dai ya karyata rade-radin da ke yawo na cewa ana shirin tsige Gwamnan.

Kwanan nan aka samu labarin cewa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya rubuta wata wasika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yake kiran sa da yayi maza yayi wasu gyara a mulkin sa kafin abubuwa su gama cabewa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel