Akwai rikici tsakanin mutanen Buhari Inji wani Sanata

Akwai rikici tsakanin mutanen Buhari Inji wani Sanata

Wani Sanata mai wakiltar Jihar Kaduna ya bayyana abin da ya sa Majalisa ta ki amincewa da Ibrahim Magu. Majalisar Dattawa ta ki amincewa ta tantace Magu bisa wasu zargi daga Hukumar DSS

Sanata Shehu Sani da Buhari

Akwai rikici tsakanin mutanen Buhari Inji Sanata Shehu Sani

Sanata Shehu Sani mai wakiltar Yankin Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa yace akwai rikici tsakanin mutanen da ke zagaye da shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sanata Sani yace wadannan mutane ne sanadiyar kin tantance Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC.

Shehu Sani yace ana buga yaki ne tsakanin mutanen da ke zagaye da shugaban kasa wanda dole sai shugaba Buhari ya bi a hankali ka da wadannan mutane ka da su ga bayan sa.

KU KARANTA: Yan Sanda sun yi wani babban kamu

Akwai rikici tsakanin mutanen Buhari Inji wani Sanata

Akwai rikici tsakanin mutanen Buhari Inji wani Sanata

Sanatan yace akwai wasu mutanen da ba na kwarai ba da ke tare da shugaba Muhammadu Buhari wanda ka iya kawo masa matsala babba a Gwamnati. Hakan ta sa wasu ma dai suke ganin cewa an karbe Gwamnatin shugaba Buharin.

Wancan makon ne dai Sanotocin Najeriya su ka ki amincewa da Ibrahim Magu a matsayin shugaban Hukumar EFCC mai yaki da zamba na din-din-din. Mafi yawan Sanatocin dai ba su yarda a nada Magu a matsayin shugaban EFCC din ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel