Zagon kasa aka yi min – Magu ya fadawa Buhari

Zagon kasa aka yi min – Magu ya fadawa Buhari

- Mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ya fadawa shugaba Buhari cewa bait aba laifi a matsayin ma’aikacin hukumar ba

- A jawabin da ya bayar, Magu ya musanta maganan cewa ya zauna a gida mai kimanin kudi N800 million kamar yadda DSS tayi ikirari

Zagon kasa aka yi min – Magu ya fadawa Buhari

Zagon kasa aka yi min – Magu ya fadawa Buhari

Magu ya fadawa shugaba Buhari a martanin da yayi kan tuhumar da akayi masa inda yace babu abinda yayi ba daidai ba.

Bayan majalisar dattawa taki tabbatar da karo na biyu a ranan Alhamis, 16 ga watan Maris, jaridar Premium Times ta bada rahoton cikakken abinda shugaban EFCC ya fadawa shugaba Buhari akan tambayar da Buhari ya masa na tuhume-tuhumen da DSS ke masa.

KU KARANTA: Kotu ta baiwa EFCC kyautan kudi

Game da cewan rahoton, Magu yace takardun da aka gani a gidansa na bincike lokacin da Mrs Farida Waziri ta bada umurnin a bincikesa, yace ba da gangan ya kaisu gida ba.

Yace: “Takardun da aka gani a gida na cikin jakan ofishina aka gani inda nike ajiye takardun da suka shafi bincike.

“Ina da niyyan baya da su ne. ba daidai bane ace da gayya na ajiye takardun EFCC a gida na.

“Kana kuma, ina son ka sani cewa wasunmu da sukayi aiki tare da Ribadu mun sha bakar wahala bayan tafiyarsa.”

Magu ya musanta cewa shin a hannun daman tsohon shugaban hukumar, Ibrahim Lamorde ne kuma yana amfani da shi wajen cin mutuncin mutane.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel