Shugaban kungiyar Boko Haram, Shekau, ya fito a sabon bidiyo

Shugaban kungiyar Boko Haram, Shekau, ya fito a sabon bidiyo

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya bayyana a wani sabon bidiyo da aka saka a ranar Juma’a, ya karyata hare-haren da aka kai Libya kwanan nan, yayinda ya yi barazana ga shugabannin duniya.

An nuno Shekau inda yake godiya ga mabiyan sa, a cikin bidiyon mai tsawon mintuna 27, da wani dan jarida mai alaka da Boko Haram ya tura wa jaridar Premiym Times.

KU KARANTA KUMA: An kama dan Boko Haram kurma kuma bebe dauke da wayoyi 8

Shekau ya nuna katin shaidar sa, makamai, alburusai da sauran kayayyakin da ya kwata daga hannun sojojin Kamaru.

Har ila yau Shekau ya umarci mayakansa da su gyara damtse, ya kara da cewa yan ta’addan bazasu ja bay aba har sai an kafa sharia a Benin, Kamaru, Chadi, Nijar, Najeriya da kuma Mali.

Bidiyon na zuwa ne kwanaki uku bayan kungiyar ta’addan tayi ikirarin kashe wasu yan leken asirin gwamnati guda uku a cikin wani bidiyo da ta saki.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel