Wani bincike ya nuna Shugaba Buhari ne wanda aka fi so a Najeriya

Wani bincike ya nuna Shugaba Buhari ne wanda aka fi so a Najeriya

Soyayyar da talakawan Nijeriya ke nuna wa Shugaba Muhammadu Buhari, na ci gaba da ba masana harkokin siyasar kasar nan da ma duniya mamaki, musamman da suke ganin ko mai wuya ko mai dadi, wadanda suka yi tururuwar zabarsa a shekarar 2015, har yanzu ba su janye goyon bayan da suke ba shi ba.

Wani bincike ya nuna Shugaba Buhari ne wanda aka fi so a Najeriya

Wani bincike ya nuna Shugaba Buhari ne wanda aka fi so a Najeriya

Makon da ya gabata, aka fitar da sanarwar dawowar shugaba Muhammadu daga kasar Ingila bayan ya shafe tsawon kwanaki 51 yana hutawa, inda ya yi amfani da wannan dama domin Likitoci su duba lafiyarsa.

Jim kadan bayan sanarwar da ta fito daga bakin Babban Mai Taimaka masa ta fuskar Yada Labarai, Mista Femi Adeshina, ‘yan Nijeriya suka fara fitowa kwansu da kwarkwata don nuna farin cikinsu na dawowar Shugaba Buhari; tun a daren ranar dawowar tasa, wasu suka yi wa filin sauka da tashin jiragen sama na Kaduna tsinke domin su yi tozali da shi, su yi masa lale marhabin.

KU KARANTA: Mulkin Najeria na nema yafi karfin Shugaba Buhari

Dubun dubatar al’ummar Hausawa, Yarbawa da Inyamurai, sun nuna farin ciki da jin dadinsu na dawowarsa. Tambayar da mutane ke yi kansu shi ne, me ya sa ake yi wa Shugaba Muhammadu Buhari irin wannan soyayyar? Me ya sa duk da matsin tattalin arzikin da ake cewa Nijeriya na ciki, amma talakawa ba su kosa ba? Wace kididdiga ce ta nuna ya fi kowa farin jini a yanzu?

Irin soyayyar da talakawa ke nuna wa Shugaba Muhammadu Buhari dole ta razana masu adawa da shi, musamman da yanzu ake tunkarar shekara ta karshe wadda daga ita sai zabe. Masana harkokin siyasa na da ra’ayin cewa matukar wannan Dattijon ya sake tsayawa takara, babu shakka zai iya lashe zaben Shugaban Kasa a karo na biyu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel