Jiga jigan ýan Boko Haram su 9 sunyi saranda ga sojojin Najeriya

Jiga jigan ýan Boko Haram su 9 sunyi saranda ga sojojin Najeriya

Rundunar mayakan sojan kasa ta kara samun wata gagarumar nasara a yakinta da kungiyar ta’addanci, inda a jiya Alhamis 16 ga watan Maris wasu jiga jigan yan Boko Haram su 9 suka mika wuya ga sojoji.

Jiga jigan ýan Boko Haram su 9 sunyi saranda ga sojojin Najeriya

Jiga jigan ýan Boko Haram su 9 sunyi saranda ga sojojin Najeriya

Daraktan watsa labarai na rundunar Birgediya SK Usman ne ya bayyana haka inda yace jiga jigan yan Boko Haram din sun 9, yan kauyen Tambashe ne dake karamar hukumar Dikwa na jihar Borno.

KU KARANTA: An rushe mafakar mayaƙan Boko Haram a jihar Kogi (Hotuna)

“Yayin da ake samun wasu mutane marasa kishi suna boye yan Boko Haram don su cigaba da kai hare hare, wasu kuwa daga cikin yan ta’addan sun fahimci basu da wani wurin fakewa, don haka suka kawo kansu.

“A kwanaki 2 da suka gabata ne, wasu yan Boko Haram su 9 daga kauyen Tambashe na karamar hukumar Dikwa suka kawo kansu da kansu ga sojojin dake jibge a tsakanin hanyar Dikwa da Gulumba Gana.

“Yan Boko Haram din sunce sun gaji da halin da suke ciki a kungiyar ta Boko Haram, don haka ne suka mika wuya tare da tuba, amma duk da haka, ana cigaba da binciken mutanen” inji SK Usman.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel