Muna bayan Shugaba Buhari 100%-Rundunar Soji

Muna bayan Shugaba Buhari 100%-Rundunar Soji

Sabon Darektan yada labarai na Rundunar Sojin Najeriya ya bayyana abin da ya hana Najeriya wargajewa, a cewar sa Gidan Sojin ne

Muna bayan Shugaba Buhari 100%-Rundunar Soji

Muna bayan Shugaba Buhari 100%-Rundunar Soji

A cewar Manjo Janar John Enenche Sabon Darektan yada labarai na Rundunar Sojin Najeriya Sojin kasar ne ya hana Najeriya wargajewa tun tuni. Janar din yace Sojojin Najeriya ne suka rike kasar gam suka hana ta rabewa.

Manjo Janar Enenche ya bayyanawa manema labarai a hedikwatar Sojin kasar cewa kokarin Sojojin Najeriya ne ya hana kasar wargajewa. Janar din yace Sojoji ne suka rike kasar suka kuma kare ta daga masu tada kayar baya. Darektan Sojin yayi tir da yadda wasu Sojoji suka kasa fita yaki da ‘Yan Boko Haram a baya.

KU KARANTA: Mun yi kuskure Inji Jam'iyyar adawa

Muna bayan Shugaba Buhari 100%-Rundunar Soji

Muna bayan Shugaba Buhari 100%-Rundunar Soji

Janar Enenche yace ba don karfin Sojin Najeriya ba da tuni kasar ta rabe kamar yadda aka yi a sauran wurare a Duniya. Sabon Darektan Sojin ya kuma jaddada cewa Rundunar Sojin kasar suna bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari ya taba fadawa masu aikin hidimar kasar cewa babu wata maganar Biyafara, a manta da ita! Buhari yace a lokacin yakin ba-sasa yana kwamanda Soji, ya taka kafa-ya-kafa tun daga Arewa har can kasar kudu domin Najeriya ta zauna daya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel