Hukumar EFCC ta damke wani Shehin karya

Hukumar EFCC ta damke wani Shehin karya

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci a Najeriya ta kama wani mai suna Sheikh Saheed Omoniyi a Garin Ibadan bisa ga laifin zamba

Hukumar EFCC ta damke wani Shehin karya

Hukumar EFCC ta damke wani Shehin karya

EFCC mai yaki da cin hanci a Najeriya tayi ram da wani mai suna Sheikh Saheed Omoniyi bisa ga laifin zamba cikin aminci inda yake cutar mutane a yanar gizo da sunan cewa shi malami ne na Allah.

Wani Jami’in EFCC na Yankin Kudu ya bayyana haka ga manema labarai a Yau Alhamis. Ayo Oyewole yace Mista Omoniyi mai shekaru 24 ya saba damfarar mutane tun ba yau ba. Matashin yana yaudarar Jama’a da cewa shine babban Malamin nan na Legas Sheikh Sulaiman Onikijipa.

KU KARANTA: Magu: Sanata Ndume yayi kaca-kaca da Majalisa

An dai gano cewa wannan matashi yayi sama da kudin Jama’a har fiye da Naira Miliyan 11 inda yake fakewa da sunan wani Babban Shehi, An damke wannan mutumi ne yayin da yake hanyar zuwa Bankin bayan ya damfari wani.

Haka kuma Sanata Ali Ndume yayi kaca-kaca da Majalisa bayan ta ki amincewa ta tantace Magu bisa wasu zargi da Hukumar DSS tayi a kan sa. Ndume yace idan har haka ake aiki to da Bukola Saraki bai dace ya zama shugaban Majalisar ba don shi ma ana zargin sa da laifi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel