Yaƙi da cin hanci da rashawa: “Kada ka tausaya ma ɓarayin gwamnati” - Obasanjo ga Buhari

Yaƙi da cin hanci da rashawa: “Kada ka tausaya ma ɓarayin gwamnati” - Obasanjo ga Buhari

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba 15 ga watan Maris cewa kada ya tausaya ma barayin gwamnati, ba sani ba sabo.

Yaƙi da cin hanci da rashawa: “Kada ka tausaya ma ɓarayin gwamnati” - Obasanjo ga Buhari

Yaƙi da cin hanci da rashawa: “Kada ka tausaya ma ɓarayin gwamnati” - Obasanjo ga Buhari

Obasanjo ya bayyana haka ne yayin bikin kaddamar da fara taron kara ma juna sani na kwana 5 da tsangayar ilimin zane zane na jami’ar Ibadan dake Oyo ta shirya.

Obasanjo yace tona asirin barayin gwamnati shine hanyar da zata kawo cigaba mai daurewa kasar nan da wuri. Obasanjo ya samu wakilcin mataimaki a gidauniyar karatu ta Olusegun Obasanjo, Ayodele Aderinwale.

KU KARANTA: Majalisar dattawa taƙi amincewa da naɗin Magu a matsayin shugaban EFCC

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasar yace muddin dai ana so nahiyar Afirka ta wuce sa’a ta bangaren cigaba, shuwagabanni na bukatar tashi tsaye wajen yaji da cin hanci.

“Ba sani ba sabo wajen fallasa barayin gwamnati, dole ne mutanen kirki masu kishin kasa su bayyana kawunansu don samun mukamai na siyasa don su taimaka wajen cigaba tattalin arziki tare da samar da ingatattu ababen more rayuwa.

“Suma jama’an nahiyar Afirka dole ne a kansu dasu dage wajen matsa ma shuwagabanninsu don su yi musu hidima na gari, ko a gudu a tsira tare. Akwai bukatar aiki tare tsakanin cibiyoyin Ilimi da sauran al’umma don ciyar da nahiyar Afirka gaba.

“suma shuwagabannin siyasa dole su samar da wani tsari da zai inganta tare da samar da ababen more rayuwa. Bugu da kari ya kamata a kalli matsalar arzikin ma’adanan kasa kallo irin na adalci don samar ma al’ummar dake zaune a yankunan tagomashi.

“Daga karshe, ina tabbatar muku cewa zamu samu sauyi na gari a rayuwanmu idan muka gyara kawunan mu, wannan ba wai abune da ba zai yiwu ba."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel