Rayoyin manyan lauyoyi game da kin tantance Magu (Karanta)

Rayoyin manyan lauyoyi game da kin tantance Magu (Karanta)

Biyo bayan kin tantance Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa watau Economic Financial Crimes Commission (EFCC), manyan lawyoyi da dama sunyi tsokaci game da matsayin hakan a mahanga ta tsarin mulkin kasa.

Rayoyin manyan lawyoyi game da kin tantance Magu (Karanta)

Rayoyin manyan lawyoyi game da kin tantance Magu (Karanta)

1. Lokacin sa a EFCC ya zo karshe - inji Mike Ozekhome (SAN)

A cewar wannan babban lawyan, yanzu kam dukkan alamu sun tabbata cewa lokacin sa (Magu) ya kare a hukumar. Za a iya sanin hakan idan har aka yi duba da yadda majalisar ta dattijai ta yi watsi da zancen tabbatar da shi din. A cewar sa, idan har shugaba Buhari ya dage kan cewar sai shi din ne zai shugabanci hukumar to tabbas hakan zai saka shakku cikin zuciyar al'umma.

2. Buhari zai iya ja ma kansa idan ya dage sai Magu - JB Daudu

Shi kuwa a nashi matsayin tsohon shugaban kungiyar lawyoyin Najeriya Nigerian Bar Association (NBA) watau Joseph Daudu SAN cewa yayi hakika lokacin Magu a EFCC ya kare kuma dukkan abun da yayi daga yanzu haramtacce ne a hukumar. JB Daudu ya kuma cewa sake tura sunan Magu domin tantancewa zai iya jefa shugaba Buhari cikin matsala.

Rayoyin manyan lawyoyi game da kin tantance Magu (Karanta)

Rayoyin manyan lawyoyi game da kin tantance Magu (Karanta)

3. Magu yayi kokari sosai amma... Sebastine Hon

A cewar wannan babban lauyan kuma, Sebastine yace a nashi ra'ayin tabbas Magu yayi kokari sosai a aikin sa kuma ya cancanci tabbatar wa daga majalisar dattijan.

Sebastine ya ci gaba da cewa amma kasantuwar hukumar DSS wadda kuma take yin binciken kwakwaf kan mutane sun ce bai da gaskiya, to tabbas maganar tasu akwai kamshin gaskiya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel