An rushe mafakar mayaƙan Boko Haram a jihar Kogi (Hotuna)

An rushe mafakar mayaƙan Boko Haram a jihar Kogi (Hotuna)

Gwamnatin jihar Kogi ta rugurguza wasu gidaje a jihar inda yayan Boko Haram suke fakewa don kaddamar da hare harensu.

An rushe mafakar mayaƙan Boko Haram a jihar Kogi (Hotuna)

Gwamna Yahaya

Kakakin gwamnatin jihar Petra Akinti Onyegbule ce ta bayyana cewar an rushe wani masallaci mallakan yan ahlussunnah dake Inike cikin karamar hukumar Okene wanda yan Boko Haram suka kwace. Inda tace ko a shekarar 2015, sai da akayi karambatta tsakanin sojoji da yan Boko Haram din a wannan wurin.

KU KARANTA: Yansanda sun sace tare da yin garkuwa da jami’an zabe yan bautan ƙasa a jihar Ribas

An rushe mafakar mayaƙan Boko Haram a jihar Kogi (Hotuna)

Ana rushewa gidagen

Gwamna Yahaya Bello wanda ya samu rakiyan kwamishinan yansandan jihar Mista Wilson Inalegwu tare da sauran shugabannin hukumomin tsaro sun rushe ginin, inda ake zargin yayan Boko Haram, yan fashi da sauran miyagun mutane ke amfani da shi wajen aikata aika aiaka a karamar hukumar Okene.

An rushe mafakar mayaƙan Boko Haram a jihar Kogi (Hotuna)

An hallaka boyewar yan ta'addan

Su dai wadannan gine gine na wani mutum ne mai suna Alhaji Tijani Bakare, yayin da daya masallacin da aka rushe kuma na Ahlussunnah ne, amma Boko Haram suka kwace shi tun a shekara 2015, kua suka mayar da shi hedikwatar su.

Gwamnan yace ba zai ji tausayin duk wani mai aikata miyagun laifuka ba, kuma yace zai tabbatar da ya kaddamar da dokar yaki da garkuwa da mutane, fashi da makami da ta’addanci.

An rushe mafakar mayaƙan Boko Haram a jihar Kogi (Hotuna)

An rushe mafakar mayaƙan Boko Haram a jihar Kogi (Hotuna)

Yahaya Bello yace duk wanda aka kama da hannu cikin laifukan nan, yayi kuka da kansa, kuma doka zata hukunta shi ba sani ba sabo. “Duk wanda aka kama yana taimaka ma miyagun mutane, zamu hukunta kamar yadda ake hukunta barayin kansu.”

An rushe mafakar mayaƙan Boko Haram a jihar Kogi (Hotuna)

A gaban gidajen yan ta'addan

Gwamnan yace za’a cigaba da rusa kadarorin duk wasu masu aikata miyagun laifuka. Shima kwamishinan yansandan jihar yace zasu sanya wando daya da duk wasu masu aikata miyagun laifuka a jihar, kuma yace wannan sako ne ga masu garkuwa da mutane da sauran miyagun mutane da su gyara halayensu, tun kafin su shiga hannu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel