YANZU YANZU: Shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali ya isa majalisa cikin kayan gida

YANZU YANZU: Shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali ya isa majalisa cikin kayan gida

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban hukumar kwastam na Najeriya Kanal Hameed Ali (mai ritaya) ya take dokar majalisar dattawan Najeriya cewa ya gurfana a gaban manyan yan majalisa sanye da kayan gida.

YANZU YANZU: Shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali ya isa majalisa cikin kayan gida

Shugaban hukumar kwastam, Kanal Hameed Ali ya isa majalisa sanye da kayan gida

Hakan ya saba ma umurnin da majalisa ta bayar wanda ta nace kan cewa lallai ya zama dole ya gurfana a gaban yan majalisa cikin shigar inifam sanye da matsayinsa na shugaban hukumar.

KU KARANTA KUMA: Hukumar soji ta gargadi jama’a kan boye yan Boko Haram

Ku tuna cewa an samu hargitsi a majalisar dattawa a ranar Laraba, 15 Maris Ali ya ki zuwa kiran da majalisar tayi masa amma sai ya aika da wani wasika a maimakon haka yace ba zai samu gurfana a gaban yan majalisa saboda wani uzuri.

Amma sanatoci sukayi watsi da hakan sannan sukayi kira ga shugaban majalisar da ya sa Ali ya gurfana a gaban majalisa a ranar Alhamis, 16 ga watan Maris ko kuma a kama shi.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel