Dakarun soja sun kai ma Boko Haram harin kwantan ɓauna

Dakarun soja sun kai ma Boko Haram harin kwantan ɓauna

Wata sanarwar daga bakin kaakakin rundunar sojan Najeriya kanal Sani Usman Kuka Shekau ta bayyana cewar sojojin runduna ta 151 ta kai harin kwantan bauna ga mayakan Boko Haram yayi da suke kan wani sintiri akan titin Bama zuwa Ngurosye.

Dakarun soja sun kai ma Boko Haram harin kwantan ɓauna

Dakarun soja sun kai ma Boko Haram harin kwantan ɓauna

Sanarwar tace “Runduna ta 151 ta kai wani harin kwantan bauna da yammacin ranar Talata ga wasu mayakan Boko Haram a yayin da suke hanyarsu ta tserewa daga jihar Borno.

“Sojojin sun kashe yan Boko Haram 4, kuma sun kwato makamai da suka hada da bindiga guda 1, kirar AK 47, alburusai, makamai, bindiga kirar AK 56 guda 3, layin waya guda 5, kekuna guda 5 da tutan Boko Haram guda 1.”

KU KARANTA: Majalisar dattawa taƙi amincewa da naɗin Magu a matsayin shugaban EFCC

A wani hannun kuma, kasar Kamaru tace ta ceto sama da mutane 5000 wadanda Boko Haram suka kama, kaakakin gwamnatin kasar Kamaru Issa Tchiroma ya bada sanarwar cewar sojojin kasar Kamarun sun kai wani samame a kan iyakar kasashen Kamaru da Njeriya a ranar 27 ga watan Feburairu zuwa 7 ga watan Maris.

“Harin da muka kai ya sanya mun ceto mutane 5000 da Boko Haram ta kama, yawancin mutane da muka ceto mata ne da kananan yara, sai tsofaffi, wadanda muka kaisu sansanin yan gudun hijira dake garin Banki”

Kaakakin yaci gaba da faddin “Mun kashe sama da yayan Boko Haram guda 60, tare da kama 21”

Dakarun soja sun kai ma Boko Haram harin kwantan ɓauna

Sojoji sun kwace wasu kekuna daga yan kunar bakin wake

Dakarun soja sun kai ma Boko Haram harin kwantan ɓauna

Kekuna da an amshi daga yan ta'addan

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel