Gargadi: hukumar soji zata gwada abubuwan fashewa, sun gargadi mazauna yankin

Gargadi: hukumar soji zata gwada abubuwan fashewa, sun gargadi mazauna yankin

Hukumar sojin Najeriya ta ce zata fara lalata makamai da harsasan da ta kwato daga hannun tubabbun yan bindiga da yan kungiyar asiri na Rivers a ranar Alhamis.

Gargadi: hukumar soji zata gwada abubuwan fashewa, sun gargadi mazauna yankin

Kanal Aminu Iliyasu, kakakin hukumar soji, na mararraba 6, Port Harcourt ya bayyana hakan a Port Harcourt a ranar Laraba.

Iliyasu a wata sanarwa ya bayyana cewa za’a tayar da abubuwan fashewa da aka kwace daga tsofaffin yan bindiga sannan ya kuma kira ga mazauna yankunan da su yi taka tsantsan.

“Sashi na 6 tare da handin gwiwar kungiyar Amnesty na jihar Rivers suna bayar da sanarwan cewa zasu fara lalata makamai, harsasai da abubuwan fashewa da ka kwato daga tubabbun yan bindiga.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya lalata asibiti bayan an fada masa cewa mahaifiyarsa ta mutu

“Aikin wanda za’a fara a ranar Alhamis, 16 ga watan Maris za’a kuma gama a ranar Juma’a, 17 ga watan Maris, zai gudana a Igwuruta Army Range daga karfe 6 na safe zuwa karfe 5 na yamma a kullun.

“Har ila yau, za’a gudanar da gwajin abubuwan fashewa a tsakanin sashi na 6, sansanin sojojin Port Harcourt, a daidai wannan lokacin.

“Hukumar sun bukaci mazauna yankin, da manoma a tsakanin yankunan guda biyu da karda su tsorta idan suka ji karan fashewar abubuwa kamar yadda gwanaye zasu kula da su,” inji shi.

Iliyasu ya shawarci mazauna yankin da su kuji zuwa guraren da ake gudanar da aikin a lokacin da ake aikin.

Kakakin na hukumar sojin ya ce ana sa ran cewa Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike zai halarci gurin aikin don gani da ido.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel