Yansanda sun sace tare da yin garkuwa da jami’an zabe yan bautan ƙasa a jihar Ribas

Yansanda sun sace tare da yin garkuwa da jami’an zabe yan bautan ƙasa a jihar Ribas

Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya zargi jami’an hukumar yansandan Najeriya da takwarorinsu na sauran hukumar tsaro da aikata aika aika yayin zaukan mai mai da aka yi a jihar a ranar 10 ga watan Disamba.

Yansanda sun sace tare da yin garkuwa da jami’an zabe yan bautan ƙasa a jihar Ribas

Yansanda sun sace tare da yin garkuwa da jami’an zabe yan bautan ƙasa a jihar Ribas

Wike ya bayyana haka ne a fadar gwamnatin jihar, a garin Fatakwal yayin dayake ganawa da shugaban hukumar masu bautan kasa reshen jihar Ribas Omotayo Adewoye a ranar Talata 14 ga watan Maris, inda yace wasu yansanda sun yi garkuwa da wasu ma’aikatan zabe yan bautana kasa.

Gwamnan ya nuna damuwarsa da yadda NYSC din taki fitowa a fili ta bayyana ma duniya gaskiyar abinda ya faru.

KU KARANTA: ‘Ɗan N50m ɗin da Makarfi ke samu a hannun gwamnoni ne yasa bai son sulhu a PDP’ – Modu Sheriff

“Ba za’a taba samun zaben gaskiya da gaskiya a Najeriya ba muddin IG Ibrahim Idris ne babban sufeton yansanda, lallai sai yansanda sun canza halayyarsu zamu samu zabuka mai inganci.

“Saboda wannan sufeton yansandan yana tunanin hanyar da zai iya bi ya cigaba da rike mukaminsa kadai itace ta hanyar yi ma jam’iyyar APC magudin zabe.” Inji Wike.

Gwamnan yace ba zasu bari magudin zaben da yansanda suka shirya a jihar ya sake maimaituwa ba a jihar, saboda a yanzu jama’an Ribas sun gano shirinsu. Yace jihar Ribas na zaman lafiya tun bayan kammala zaben, inda yace da gangan aka shirya rikicin daya faru a jihar, don yansanda su samu hanyar yin magudin zabe.

A wani labarin kuma jami’an hukumar INEC da ake zargi da amsan cin hanci da rashawa sun bayyana gaban kotu a ranar Talata 14 ga watan Maris.

Jami’an INEC din su 23 sun bayyana gaban babban kotun birnin tarayya Abuja ne, inda ake tuhumarsu da aikata laifin zamba da karbar cin hancin na naira miliyan 350, wanda hakan ya saba ma dokokin safarar kudade na shekarar 2011, da kuma dokokin EFCC na shekarar 2004.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel