‘Ɗan N50m ɗin da Makarfi ke samu a hannun gwamnoni ne yasa bai son sulhu a PDP’ – Modu Sheriff

‘Ɗan N50m ɗin da Makarfi ke samu a hannun gwamnoni ne yasa bai son sulhu a PDP’ – Modu Sheriff

Rikicin cikin gida daya dabaibaye jam’iyyar PDP ya dauki sbaon salo a ranar Litinin 13 ga watan Maris, inda bangarorin biyu karkashin shugabancin Sanata Ahmed Makarfi da Sanata Modu Sheriff ke zargin juna kan tatsar jam’iyyar.

‘Ɗan N50m ɗin da Makarfi ke samu a hannun gwamnoni ne yasa bai son sulhu a PDP’ – Modu Sheriff

‘Ɗan N50m ɗin da Makarfi ke samu a hannun gwamnoni ne yasa bai son sulhu a PDP’ – Modu Sheriff

Sheriff ne dai ya fara aika ka naushi, inda zargi Makarfi da moran wasu makudan kudade a duk wata da suka kai N50m wanda wasu gwamnonin jam’iyyar ke bashi don tafiyar da jam’iyyar.

Mataimakin Sheriff Cairo Ojougboh ne ya bayyana hakan, inda yace burin Makarfi na zama dan takarar shugaban kasa ne yasa baya kaunar ganin anyi sulhu, kamar yadda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bukata.

KU KARANTA: Kwankwaso yayi bankwana da jam’iyyar APC ya koma PDP

Cairo yace: “Dalilin daya sa su Makarfi basa son ganin anyi sulhu shine saboda yadda suka ga duk sauran rassan jam’iyyar suka amince da batun sulhu, don haka Makarfi yana asarar magoya baya, musamman yadda yake ganin zai yi asarar naira miliyan 50 dayake samu duk wata daga hannun gwamnonin jam’iyyar.

“Na biyu kuma, Makarfi na tsara yadda zai shirya taron jam’iyya wanda zai yi daidai da bukatarsa na tsayawa takarar shugaban kasar nan a 2019. Muna sane da duk shirye shiryensa, don haka ba zamu bari jam’iyyar mu ta dogara akan wani mutum baya ba.

“Wannan ne ya sa shugaban mu Sheriff yace, zan baiwa kowa dama a jam’iyyar nan, kuma da wannan ne muke nazari kan matsayar kwamitin sulhu da aka kafa, muna sa ran hakan zai kawo cigaba a jam’iyyar”

Sai dai bangaren Makarfi ma ba kanwar lasa bane, inda suka mayar da martani ta bakin Kaakakinsu Dayo Adeyeye inda yace: “Sanannen abu ne ga duk wani mai ruwa da tsaki a jam’iyyar nan cewa muna fama da matsalar karancin kudi, hakan ne ma yasa bama iya biyan albashin N18m a duk wata, don haka babu wasu kudi da ake baiwa shugaban jam’iyya.

“Duk da haka, gwara a ce muna tallafa ma jam’iyyar mu da kudin yayanta, ba kamar yadda wasu gwamnonin APC da ministoci ke siya ma Sheriff mota ba, shima gwamna Fayose ya taba yin zargin cewa Sanata Sheriff ya karbi dalan amurka miliyan daya daga APC don shirya taron jam’iyya, amma Sherif bai karyata hakan ba.”

“Mun gamsu da matakin da tsohon shugaban kasa Goodlcuk Jonathan da gwamnonin jam’iyyar suka dauka na magance matsalar jam’iyyar. Matakin kuwa bai wuce Sheriff yayi murabus ba, ta yadda za’a samu yanayi mai kyau na yin zabe tareda gina aminci tsakanin yayan jam’iyyar, sai kuma mu jira hukuncin kotun koli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

“Amma Sheriff yaki yarda, ya dage lallai sai ya shirya taron jam’iyya ba tare da yayan jam’iyyar sun gamsu da shi ba. Da wannan zaku iya gane waye keda wata manufa a zuciyarsa, ina tabbatar muku cewa Sheriff ne

“Muna so Sheriff ya bamu amsa, wai menene yasa yake tsoron shari’ar kotun koli? Muna ganin bai kamata ba ace yana gudun sammaci daga kotun koli, mutum kamarsa wanda ya ci ribar hukunce hukuncen kotuna. Muna bashi shawara daya karbi sammacin kuma mu hadu a kotu.”

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel