YANZU-YANZU! Alkaluma sun nuna faduwar farashin kayayyaki a karon farko a watanni 15

YANZU-YANZU! Alkaluma sun nuna faduwar farashin kayayyaki a karon farko a watanni 15

- Hukumar kididdiga ta kasa batau National Bureau of Statistics NBS, ta fitar da wani rahoto da ke nuna cewa 'farashi' ya sauka sosai a Najeriya, inda hakan ke nuna cewa tattalin arzikin kasar ya fara farfadowa

- Hukumar NBS ta ce hauhuwar farashin ya sauka daga kashi 18.72 cikin 100 da yake a watan Janairu zuwa kashi 17.78 cikin 100 a watan Fabrairun 2017

YANZU-YANZU! Alkaluma sun nuna faduwar farashin kayayyaki a karon farko a watanni 15

YANZU-YANZU! Alkaluma sun nuna faduwar farashin kayayyaki a karon farko a watanni 15

Duk da raguwar farashin, adadin hauhawar farashi yana nan a matakin da yake, wanda shi ne mafi yawa tun zamanin mulkin shugaba Olusegun Obasanjo.

A hannu guda kuma, Bankuna a Najeriya na neman mutanen da za su sayi dala ruwa a jallo, inda suka ce a yanzu suna da kudaden kasashen wajen da dama da babban bankin kasar CBN, ya basu.

KU KARANTA: Darajar Naira ta karu bayan dawowar Buhari

Masu sharhi da dama na ganin tun da a yanzu bankuna na 'neman kai' da kudaden kasashen wajen, hakan na iya daga darajar Naira, ya kuma rage wawagegen bambancin da ke tsakanin musayar dala da naira a kasuwanni bayan fage da bankuna.

Najeriya dai tana fama da matsalar rashin isassun kudaden kasashen waje, al'amarin da ya jawo hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa ga 'yan kasar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel