Hamid Ali ya gana da Bukola Saraki

Hamid Ali ya gana da Bukola Saraki

An ga Hamid Ali watau shugaban Hukumar fasa-kauri na kasa a harabar Majalisa inda yaje ya gana da Dr. Bukola Saraki da yamma

Hamid Ali ya gana da Bukola Saraki

Hamid Ali ya gana da Bukola Saraki

Shugaban Hukumar kwastam na kasa Kanal Hamid Ali mai ritaya ya taka zuwa Majalisa inda ya gana da shugaban Majalisar dattawa na kasar watau Bukola Saraki salin-alin a Ofishin sa kamar yadda rahotanni suka nuna.

Hamid Ali ya leka Majalisar ne a jiya da yamma ya kuma bar Majalisar kimanin karfe 6:00. Idan ba a manta ba dai Sanatocin Najeriya sun gayyaci shugaban kwastam na kasa zuwa Majalisar inda suka ce kuma dole sai ya sa kayan hukumar.

KU KARANTA: An kai harin bam a Maiduguri

Hamid Ali ya gana da Bukola Saraki

Hamid Ali ya gana da Bukola Saraki

Da alamu dai shugaba Buhari ne ya tursasa Hamid Ali da ya je Majalisar ya amsa kiran da suke yi masa. A baya dai Hamid Ali yace ba zai je Majalisar ba har sai sun bi matakan da ya dace, Hamid Ali ya kuma ce babu abin da zai sa ya saka rigar Kwastam yana tsohon Soja.

Sai dai Sanatocin sun ce idan har ta kama za su nemi a tsige Shugaban na Kwastam idan yayi mata taurin kai. Yanzu haka dai Hamid Ali ya nemi a saka masa wata rana ya je Majalisar don kuwa cewa ayyuka sun masa yawa a Ranar Laraba watau Yau.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An rufe filin saukar jirgin Abuja

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel