Atiku yayi alƙawarin daukan nauyin karatun yayan amininsa, Onukaba

Atiku yayi alƙawarin daukan nauyin karatun yayan amininsa, Onukaba

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya kaddamar da gidauniyar daukan nauyin karatun yayan hadiminsa wanda ya rasu, Dakta Adinoyi – Ojo Anakuba.

Atiku yayi alƙawarin daukan nauyin karatun yayan amininsa, Onukaba

Atiku da Onukaba

Turakin na Adamawa ya sanar da haka ne ta bakin daraktan watsa labaran ofishinsa Paul Ibe a ranar Talata 14 ga watan Maris yayin daya je yi ma iyalan mamacin ta’aziyyan sadakan bakwai.

Ibe yace manufar gidauniyar itace don tallafa ma yayan mamacin cigaba da karatunsu har zuwa jami’a.

KU KARANTA: "Abinda muka tattauna da Buhari a zaman da mukayi da shi a yau" – inji Saraki da Dogara

Atiku yayi alƙawarin daukan nauyin karatun yayan amininsa, Onukaba

Atiku yayi alƙawarin daukan nauyin karatun yayan amininsa, Onukaba

“Mai girma tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya umarce ni da in sanar ma iyalan marigayi Onukaba da cewa ya tsara wata gidauniya da zata dauki nauyin karatun yayan Dakta Adinoyi-Ojo Onukaba har zuwa jami’a” inji Ibe

Hakan da Atiku yayi, sais aura abokanan Onukaba suka kaddamar da wata kwamiti da zata tallafa ma iyalan mamacin.

Marigayi Onukaba ya rasu ne a hanyarsa ta dawowa daga bikin murnan cika shekaru 80 na Cif Olusegun Obasanjo, kuma ya mutu ya bar mata daya da yaya 4.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel