An yi gaba da sama da Dala Biliyan 15.8 a NNPC-NEITI

An yi gaba da sama da Dala Biliyan 15.8 a NNPC-NEITI

An gano cewa Kamfanin NNPC na kasa yayi sama da Dala Biliyan 15.8 bai biya asusun gwamnatin tarayya ba na wasu shekaru

An yi gaba da sama da Biliyan Dala 15.8 a NNPC-NEITI

An yi gaba da sama da Biliyan Dala 15.8 a NNPC-Inji NEITI

Hukumar NEITI ta bayyanawa manema labarai na kasa cewa Kamfanin mai na kasa watau NNPC bai maidowa gwamnatin tarayya makudan biliyoyi har sama da dala biliyan 15.8 na kudin da ya karba daga LNG ba.

Wani babban Jami’in Hukumar na NEITI Mista Peter Ogbobine ya bayyana haka a yau Talata. NEITI tace daga shekarar 2004 zuwa 2014 NNPC ba ta saka kudin a asusun gwamnati ba kamar ya dace. Hukumar dai tace ta bayyanawa gwamnati irin wannan badakalar sai tayi gum ba tace komai ba.

KU KARANTA: Majalisa ta kusa gama zama game da kasafin kudi

Dama dai can an kirkiri hukumar ne saboda sa ido game da abubuwan da ke faruwa a bangaren man fetur da gas na kasar. Ana tafka mugun badakala a fannin mai na kasar inda nan ne arzikin da kasar ta dogara.

Kwanaki Majalisar Dattawa ta bankado wata mahaukaciyar badakala a bangaren man fetur na kasar. Majalisar tace ta gano cewa manyan ma’aikatan kamfanin NNPC na kasa sun sace sama da Naira tiriliyan 10 da sunan tallafin fetur.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An kama Jami'an INEC

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel