Kwastam ta fara kamen motocin da ba a biya masu haraji ba

Kwastam ta fara kamen motocin da ba a biya masu haraji ba

- Hukumar Kwastam ta Najeriya ta fara aikin rijistar motocin da aka shigar da su kasar ba tare da biyan kudin haraji ba, abin da hukumar ke ganin tamkar zagon ‘kasa ne ga tattalin arzikin kasa.

- Shugaban hukumar kwastan Kanar Hamid Ali mai ritaya, ya ce matakin kwastam na yin rijistar motocin ba an ‘dauke shi bane da nufin gallazawa talaka, sai dai neman masu motocin da basu biya kudaden harajinsu ba kawai.

Kwastam ta fara kamen motocin da ba a biya masu haraji ba

Kwastam ta fara kamen motocin da ba a biya masu haraji ba

Kamar yadda rahotanni ke cewa jami’an hukumar kwastam za su tsare hanya suna bincikar motocin da ba a biyawa haraji ba sun kwace motocin. A cewar shugaban hukumar kwastam, wannan batu ba haka yake ba, jami’an kwastam zasu dakon masu sabunta takardun motocinsu a cibiyoyin daban-daban da ake da su a fadin ‘kasar, idan aka samu motar da ake bi haraji za a tilasta mata biya.

Tuni dai ‘yan Najeriya ke Allah wa dai da matakin hukumar Kwastam, inda suke ganin zai takurawa masu ‘karamin ‘karfi.

A cewar tsohon mataimakin shugaban hukumar Kwastam, Alhaji Ibrahim Musa Gongwazo, matakin hukumar yana bisa doka kuma zai taimaka wajen ‘karawa hukumar kudaden shiga.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel