Wurare gagarumi 7 da ya kamata a je a Arewa

Wurare gagarumi 7 da ya kamata a je a Arewa

- Fiyar da shekaru 2,500 yanzu, wannan gari yana nan kuma an san shi da sassaƙa kalakala wadda su ka fi sufa a Afirka

- Mutane na zamamani sun gano da wajen a shekara 1928. Su ka san cewar, wasu sun zauna a wurin lokacin 500BC sai kuma suka bata a 200AD

- Da safeya ta yi, mutum zai iya yawo na ganin dabbobi da kuma shan iska. Wannan yawo ake cewar, ‘morning safari

Wurare gagarumi 7 da ya kamata a je a Arewa
Wurare gagarumi 7 da ya kamata a je a Arewa

Babu shakka Arewa na da wurare masu kyau. Domin rikici da aka yawa yin a ta Arewa, mutane da yawa sun manta da wurare hutu da shan iska mai kyau da a ke da a bangaren.

Ba san Arewa da tashin hankali kawai ba, waje ne na hutu da kwanciyan hankali idan aka amfani da abubuwar da Allah ya kafa a wajen, ta hanyoyi da suka kamata.

A can baya, turawa suka yi yawa a Arewa domin zama lafiya da lumana da suka samu. A yanzu, idan ba dauki mataki ba, duk abubiwar na alheri zai zaman abin tarihi.

Don kar wannan ya faru, ya kamata mu tuna wa kanmu abubuwa masu kyau, wuraren hutu da kwanciyar hankali da akwai a wajajen Arewa.

1. NOK village:

Fiyar da shekaru 2,500 yanzu, wannan gari yana nan kuma an san shi da sassaƙa kalakala wadda su ka fi sufa a Afirka.

Mutane na zamamani sun gano da wajen a shekara 1928. Su ka san cewar, wasu sun zauna a wurin lokacin 500BC sai kuma suka bata a 200AD.

Masu aikin tono ma'adinan ƙarƙashin ƙasasuka gano da aka a shekara 1928 din. Mutane da sun zauna a da din ne ake cewa Nok.

KU KARANTA: Nayi danasanin rabuwa da tsohon mijina, dukan da nake sha yayi muni,’ wata mata ta fada ma kotu

Kauyen Nok tana jihar Kaduna kan tsayi wanda yake daidai da 160 ta Arewan Gabas na Baro.

2. Yankari:

Yankari wajen hutu na gwamnatin tarraya ne a jihar Bauchi. Shi ne na farko irin shi a Najeriya. An kafa shi a shekara 1956 ama an meda zuwa wajen dabbobi da ya fi girma a Najeriya a shekara 1991.

Wannan wajen hutu ne ake bari dabbobi suna ta yawo ba mai kashe su. Anan wurin, dabbobi sun fi mutane damar. Acikin Yankari, akwai gidaje nah utu da abubuwar kalakala na hutawa banda dabbobi da suna yawo.

Da safeya ta yi, mutum zai iya yawo na ganin dabbobi da kuma shan iska. Wannan yawo ake cewar, ‘morning safari’.

3. Wiki warm spring:

Anan ne inda ruwa yake ɓuɓɓugowa daga ƙasa acikin Yankari a jihar Bauchi. Wajen na kusa da rafin Gagi kamar tuki sa’o’I 1 1/2 a mota. Yana ta kudanci gabas na garin Bauchi.

Abin mamaki na ruwan nan shi ne, ba ta sanyi kuma ba ta zafi. Kulum, ta na nan dai dai da jiki. Ga safta, ga aske.

4. Zuma rock:

KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Ali Nuhu ya zama jakada a Najeriya?

Ka taba ga wani dutse mai ido, mai baki da hanci? Zuma rock, wani dutse mai tsawan mita 725 dake tsakanin jihar Neja da kuma babban birnin tarayya wato Abuja.

Da mutanen Zuba da Koros da ana cewa Kororofa sun sami zuma rock a wajen ne. kafin a san da Abuja, Lafia ko Keffi, mutanen Zuba suna zama a ta baban dutse nan. Da ana cewa dutsen Zumwa kafin Hausawa suka zo suka samesu suka far ace mishi zuma wato ‘zuma rock’

5. Gubi lake:

Wanan tafki na ruwa mai safta, mai aske. Mutane basu yawa sanni akwai wurin da za su iya hut aba fargaba anan ba.

6. Gurara falls:

Wurin nan ya zauna ne tsakanin Suleja da Minna duk a jihar Neja. Tukin sa’o 1 ne daga Abuja. Ruwan nan na sauka daga kan dutse zuwa kasa kuma ya yi fadin mita 200 da kuma sayin mita 30.

7. Wase rock:

Wannan dutse ne na jihar Plateau. Abin mamaki shi ne wannan dutse, idan a ka kali kamani shi, yana nan kamar dutse na zuma, ama ba ya walki kamar shi. Ya ke tsayin 450. Yana kan tsayin hanya 216 ta kudanci gabas na Jos.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel