YANZU YANZU: Boko Haram ta saki sabon bidiyo, ta kashe wasu da ake zargin yan leken asirin gwamnati ne

YANZU YANZU: Boko Haram ta saki sabon bidiyo, ta kashe wasu da ake zargin yan leken asirin gwamnati ne

Kungiyar yan ta’addan Boko Haram ta saki wani sabon bidiyo na farfaganda.

Sahara Reporters ta rubuta cewa kungiyar adawar Abubakar Shekau na Boko Haram ce ta saki bidiyon kuma cikin abubuwan da ta nuna shine kashe wasu mazaje da ake ganin yan leken asirin gwamnatin Najeriya ne da suka samu shiga kungiyar.

YANZU YANZU: Boko Haram ta saki sabon bidiyo, ta kashe wasu da ake zargin yan leken asirin gwamnati ne

Boko Haram ta saki sabon bidiyo, ta kashe wasu da ake zargin yan leken asirin gwamnati ne

Bidiyon wanda aka yi a cikin harsunan Hausa da Larabci ya kasance kamar shirin fim inda aka nuna hotunan malaman musulunci, jami’an gwamnati da shugabannin duniya harma da wani sashi dake nuna hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Donald Trump, tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama da wasu shugabannin Turai da dama.

Har ila yau bidiyon ya hada da kisan wasu mutane uku wanda kungiyar ta Boko Haram tayi ikirarin cewa sashin kwararru na hukumar sojin Najeriya ne ta dauke su aiki don su dunga leken asirin kungiyar.

An yanke ma mutanen hukuncin kisa a karshen bidiyon mai tsawon mintuna 7.

Kungiyar ta kuma nuna wasu manyan makaman sojoji wanda suka hada da harsashi masu linzami yayinda sukayi alfaharin cewa yana nan a kebabben guri da hukumar sojin Najeriya bazata iya sake kwata ba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel