Dole Buhari ya saki Dasuki da Nnamdi Kanu Inji Fayose

Dole Buhari ya saki Dasuki da Nnamdi Kanu Inji Fayose

- Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya kara caccakar shugaba Buhari

- Ayo Fayose yace ya kamata Buhari ya saki Dasuki

- Gwamna Fayose yace shugaba Buhari yayi ma Bayin Allah rahama

Dole Buhari ya saki Dasuki da Nnamdi Kanu Inji Fayose

Dole Buhari ya saki Dasuki da Nnamdi Kanu Inji Fayose

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saki Sambo Dasuki da kuma Nnamdi Kanu ba tare da wata-wata ba. Gwamnan yace bai kamata shugaba Buhari ya cigaba da rike mutane bayan Kotu ta bada izini a sake su ba.

Gwamna Ayo Fayose ya nemi shugaban kasa Buhari yayi amfani da idanun rahama ya jikan tsohon mai bada shawara game da harkar tsaro Sambo Dasuki da kuma shugaban Kungiyar IPOB mai fafutukar neman kasar Biyafara Nnamdi Kanu da ke rufe tuni.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya aika Osinbajo zuwa Neja-Delta

Dole Buhari ya saki Dasuki da Nnamdi Kanu Inji Fayose

Dole Buhari ya saki Dasuki da Nnamdi Kanu Inji Fayose

Fayose yace yadda Buhari ya samu rahamar Ubangiji ya samu sauki ya taimaka ya bada belin wadannan bayin Allah da suka dade a garkame ko da Kotu ta bada umarni a sake su. Fayose yace bai halatta gwamnati ta cigaba da rike su ba.

Kwanan nan Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Peter Fayose yayi addu’a Ubangiji ya ba shugaban kasar karfin tafiyar da mulkin yace domin yana bukatar gyara abubuwa da dama da suka tabarbare a kasar. Fayose yace za suyi ta addu’a Buhari ya sauko da farashin dala zuwa N200 sannan kuma samu saukin abinci.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Buhari ya dawo; Me 'Yan Najeriya su ke cewa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel