Neja-Delta: Shugaba Buhari ya aika Osinbajo wani aiki

Neja-Delta: Shugaba Buhari ya aika Osinbajo wani aiki

- Mataimakin shugaban kasa Osinbajo zai jagoranci tawagar gwamnati zuwa Yankin Neja-Delta

- Osinbajo ya fara wannan zagaye a lokacin da shugaban kasar yayi tafiya

- Da alamu shugaba Buhari ya ji dadin aikin Osinbajo

Neja-Delta: Shugaba Buhari ya aika Osinbajo wani aiki

Neja-Delta: Shugaba Buhari ya aika Osinbajo wani aiki

Da alamu shugaba Muhammadu Buhari ya ji dadin aikin Mataimakin sa Farfesa Osinbajo yayin da ba ya kasar. Yanzu haka dai shugaba Buhari ya nemi Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa Yankin Neja-Delta domin kawo karshen rikicin da ake ta fama da shi.

Yayin da shugaba Buhari ya tafi zuwa Landan domin ganin Likita, Osinbajo ya zagaya Yankin Neja-Delta mai arzikin mai domin kawo karshen rikicin tsageru a Yankin. Osinbajo ya leka Garuruwa da dama inda yace shugaba Buhari ne ya turo sa domin kawo karshen rikicin Yankin.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya komai Ofis

Mai ba shugaban kasa shawara game da harkokin Neja-Delta Birgediya-Janar Paul Boroh ya bayyana haka dai jiya a Abuja. Janar din mai ritaya yace Farfesa Osinbajo zai jagoranci tafiyar domin gano matsalolin Yankin na Neja-Delta da kuma kawo zaman lafiya na din-din-din.

Dama can Osinbajo ya ziyarci Jihohin Bayelsa, Edo, Ribas, da Jihar Imo. Wannan karo Mataimakin shugaban kasar zai kai ziyara ne Jihohin Kuros-Riba, Abia da kuma Jihar Ondo.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda aka tarbi Osinbajo a Neja-Delta

Neja-Delta: Shugaba Buhari ya aika Osinbajo wani aiki

Neja-Delta: Shugaba Buhari ya aika Osinbajo wani aiki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel