Abubuwan da Osinbajo yayi lokacin da shugaba Buhari ba ya nan

Abubuwan da Osinbajo yayi lokacin da shugaba Buhari ba ya nan

- Mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo ya rike Najeriya lokacin shugaba Buhari yana Landan

- Osinbajo ya aiwatar da abubuwa da dama na gyaran kasar

- Yanzu dai Osinbajo ya mika karagar mulki ga shugaba Buhari

Abubuwan da Osinbajo yayi lokacin da shugaba Buhari ba ya nan

Abubuwan da Osinbajo yayi lokacin da shugaba Buhari ba ya nan

Yayin da shugaba Buhari ya tafi zuwa Landan domin ganin Likita, Farfesa Osinbajo ya zama mukaddashin shugaban kasar. Osinbajo ya gabatar da ayyuka da dama, daga ciki:

1. Ziyarar Neja-Delta:

Osinbajo ya zagaya Yankin Neja-Delta mai arzikin mai domin kawo karshen rikicin tsageru a Yankin.

2. Tattalin arziki da kuma saukar dala:

Osinbajo yayi taro da dama domin gyara tattalin arzikin kasar har aka kuma dace farashin dala ya sauka kasa da CBN ta saki daloli ga Bankuna.

KU KARANTA: Al'ummar Ribas sun yi murnar dawowar Buhari

Abubuwan da Osinbajo yayi lokacin da shugaba Buhari ba ya nan

Abubuwan da Osinbajo yayi lokacin da shugaba Buhari ba ya nan

3. Rufe filin jirgin Abuja:

An rufe filin jirgin sama na Abuja domin yin wasu gyara inda aka koma sauka a filin jirgin da ke Kaduna.

4. Nadin Alkalin Alkalai:

A lokacin dai Farfesa Osinbajo ya tura sunan Alkali Walter Onnoghen a matsayin Alkalin Alkalai na kasar ga Majalisa inda kuma aka rantsar da shi.

5. Rikicin Kudancin Kaduna:

Osinbajo ya ziyarci mutanen Kudancin Kaduna inda ake ta fama da rikici na dogon lokaci. Osinbajo yayi jaje ga Jama’an ya kuma ce zai dawo domin kawo karshen rikicin.

A jiya Mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ya bayyana cewa ya mika ragamar mulki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari 13 ga Watan Maris. Kafin nan Osinbajo ya gana da shugaban kasa na sama da sa’a guda.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko mace na iya mulkin Najeriya?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel