Osinbajo ya mikawa Buhari mulki

Osinbajo ya mikawa Buhari mulki

- Mataimakin shuganan kasa Farfesa Osinbajo yace ya mikawa Buhari ragamar mulki

- Osinbajo ya gana da Buhari game da harkokin kasa

- An yi kusan sa’a guda ana ganawa tsakanin shugabannin

Osinbajo ya mikawa Buhari mulki

Osinbajo ya mikawa Buhari mulki

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa ya mika ragamar mulki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a Yau Litinin 13 ga Watan Maris. Kafin nan Osinbajo ya gana da shugaban kasa na sama da sa’a guda.

Mataimakin wanda ya rike kasar yayin da shugaba Buhari ba ya nan sun tattauna da shugaban na dogon lokaci inda suka yi magana game da tattalin arziki da kuma kasafin kudi da sauran sha’anin kasa.

KU KARANTA: UPDATED: Buhari resumes work, notifies National Assembly (photos)

Yemi Osinbajo zai cigaba da aikin sa a matsayin Mataimaki

Osinbajo ya mikawa Buhari mulki

Osinbajo yace shugaba Buhari ya gamsu da yadda ya gudanar da sha’anin kasar. Shugaban kasar ya kuma bada umarnin yadda za a cigaba da tafiyar da sha’anin kasar. Osinbajo dai zai koma mukamin san a Mataimakin shugaban kasa. Osinbajo ya ziyarci Jihohi da dama a lokacin inda aka kuma samu farashin dala ta sauko kasa.

Wani Dan Jarida a kasar Ingila ya bayyana yawan mutanen da shugaba Muhammadu Buhari ya tafi da su kasar Ingila inda yayi doguwar jinya na sama da watanni biyu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel