Mummunan hatsarin mota Ya kashe mutane 30 a Arewa

Mummunan hatsarin mota Ya kashe mutane 30 a Arewa

Hatsarin mota yayi sandiyar rayukan mutane sama da 30 tare da raunata wasu da yawa, kan hanyar zuwa Ngurore dake jihar Adamawa.

Mummunan hatsarin Mota Ya kashe mutane 30 a Arewa

Mummunan hatsarin Mota Ya kashe mutane 30 a Arewa

Kamar yadda bayanai ke nunawa wata babbar motar daukan kaya wato ‘Tirela’ shake da shanu da kuma dandazon matasa ce ta yi hatsari a kwanar Ngurore, inda wadanda suka shaida faruwar lamarin ke cewa fiye da mutane 30 akasari matasa suka rasa rayukansu nan take, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka.

Lamarin ya faru ne akan hanyarsu ta komawa Ngurore bayan sun ci kasuwar Song, dake arewacin jihar Adamawa. An dai garzaya da gawarwakin wadanda suka raunata zuwa manyan asibitocin jihar.

‘Yan kungiyar Union na cikin wadanda suka kai agajin farko, a wani yanayi na ban tausayi kamar yadda shugaban kungiyar na jihar Adamawa Alhaji Bello Adamu Ngurore, ya bayyanawa majiyar mu.

To sai dai kuma yayin da alkaluman wadanda suka rasu a hadarin ake tsammanin zasu iya karuwa, rundunar ‘yan sandan jihar ta bakin kakakinta SP Othman Abubakar, ta tabbatar da faruwar lamarin da kuma cewa mutune 15 ne suka rasu.

A Najeriya dai baya ga batun lalacewar hanya sau tari akan zargin direbobin manyan motocin da tukin ganganci.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel