Rundunar soji zata fara amfani da sabon usulubi wajen tabbatar da tsaro a jihar Legas da Ogun

Rundunar soji zata fara amfani da sabon usulubi wajen tabbatar da tsaro a jihar Legas da Ogun

- Rundunar sojin kashi na 81 tace zata fara fara amfani da sabon salon dakile rashin tsaro a jihohin guda biyu

Rundunar soji zata fara amfani da sabon usulubi wajen tabbatar da tsaro

Rundunar soji zata fara amfani da sabon usulubi wajen tabbatar da tsaro

Shugaban rundunar sojin wato GOC, Manjo Janar Ebenezar Oyefolu ya alanta cewa sashen sa zata fara amfani da wata sauwar usulubi wajen magance zancen rashin tsaro a jihar Legas da Ogun.

Jaridar Sun ta bada rahoton cewa Ebenezar Oyefolu ya bayyana hakan ne a wata taron kulle shirin horar da soji 100 akan sabo usulubin.

KU KARANTA: CBN zata cigaba da fito da dala har sai ya daidaita

Yace: “ Dangane da irin yan barandan da muka samu a wurin nan, wajibi ne mu canza salon yaki da su.

“Yanda muhimmanci a garemu mu san yadda zamu dakile duk wani al’amarin rashin tsaro kuma muci nasara.”

GOC din ya jinjinawa hafsoshin da suka mayar da hankali wajen horon kuma yayi kira da sus u koyar da juna idan an rabasu zuwa wajen ayyukansu.

An gudanar da wannan horo ne domin bunkasa shirye-shireyn kwamandoji da kuma ma’aikata. Kana kuma ya gargadi sojin da suka zo jihar domin horon su kasance cikin farga akoda yaushe.

A bangare guda, rundunar sojin 1 Division na jihar Kaduna, a ranan juma’a sunyi kira ga manema labarai su bayar da goyon bayansu ga soji wajen tabbatar da tsaro a kasa.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel