Ranar komawar Buhari Landan bai tabbata ba – Fadar shugaban kasa

Ranar komawar Buhari Landan bai tabbata ba – Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta ce har yanzu babu tabbacin ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai koma birnin Landan don ci gaba da magani.

Ranar komawar Buhari Landan bai tabbata ba – Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta ce shugaban kasa Buhari ya bayar da sanarwan cewa akwai bukatar ya koma Landan don ci gaba da magani

Don haka fadar shugaban kasa ta bayyana cewa koda dai ba’a tabbatar da ainahin ranar ba, shugaban kasa Buhari da likitocin sa ne zasu yanke wannan shawarar.

KU KARANTA KUMA: Manyan yan Najeriya, da kungiyoyi sun shirya manufofi ga Buhari yayinda ya koma bakin aiki

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a shafin zumunta, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a wani hira tare da Arise News Network a ranar Lahadi, 12 ga watan Maris a Abuja.

Garba ya bayyana cewa shugaban kasar ya bayar da sanarwan cewa akwai bukatar ya koma wanda ya bayyana a matsayin daidai.

Mataimakin shugaban kasar yace tunda Buhari ya dawo, duk wani dake fadar shugaban kasa ya ji sanyi a rai.

Ya ce dawowar shugaban kasa ya kasance wanke fadar shugaban kasa daga tuhuman cewa Buhari bai mutu ba kamar yadda wasu mutane ke fadi.

Da yake magana game da rahotannin dake karo game da rashin lafiyar shugaban kasa, Garba ya ce: “Kada mutun ya dunga furta abunda bai sani ba, na daya kenan.

“Na biyu, al’amurran rashin lafiya sirri ne sosai. A cikin shirye-shiryen, Femi Adesina ya samu wani dogon bayani daga ministan lafiya, Farfesa Isaac Adewole, inda ya bayyana abunda fallasa ke nufi a kimiyyar likitanci.”

Ya kara da cewa ya rage ga mara lafiya idan yana son bayyana rashin lafiyar sa, kamar yadda ko likitan ba zai iya bayyana ma kowa ba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel