Hukumar ƙidaya zata yi ƙididdigan ýan Najeriya a 2018

Hukumar ƙidaya zata yi ƙididdigan ýan Najeriya a 2018

Shugaban hukumar kidaya ta kasa (NPC), Cif Eze Duruiheoma yace aikin kididdigan jama’an kasar Najeriya da gidajensu zai gudana a farko shekarar 2018.

Hukumar ƙidaya zata yi ƙididdigan ýan Najeriya a 2018

Hukumar ƙidaya zata yi ƙididdigan ýan Najeriya a 2018

Shugaban hukumar ya bayyana haka ne a karshen makon data gabata yayin aikin tantance iyakokin garuruwa a garin Gwagwalada dake babban birnin tarayya Abuja.

Cif Eze ya bayyana cewar zuwa yanzu sun kammala shirye shiryen gudanar da aikin idan an basu dukkanin kayayyakin da suke bukata don gudanar da aikin.

KU KARANTA: Yanzun nan: Buhari ya umarci Osinbajo ya cigaba rikon kwarya, yana bukatan hutawa kadan

Hukumar ƙidaya zata yi ƙididdigan ýan Najeriya a 2018

Shugaban hukumar kidaya ta kasa (NPC), Cif Eze Duruiheoma

“Muddin muka samu dukkanin kayayyakin aikin da muke bukata, kuma aka sakar mana kudaden aiki, ina tabbatar maka da cewa zuwa farko, ko cikin kashi na biyu na shekarar 2018 zamu gudanar da ikin kidayan.” in ji shi.

A yanzu hukumar tana gudanar da aikin tantance iyakokin kasa a kananan hukumomin guda 74, sai dai ya nuna damuwarsa da cewar suna da sauran kananan hukumomi 700 da zasu tantance iyakokinsu sakamakon fama da suke yi da karancin kudade.

Shugaban hukumar yace suna bukatar naira biliyan 20 don gudanar da aikin a dukkanin fadin kasar nan.

Jagoran aikin kidayan a garin Abuja, Uwargida Nkechi Odeh ta bukaci a kara musu makonni guda 2 don karkare aikin a Gwagwalada, inda tace sun fuskanci matsalar karancin kayan aiki, hakan ya sanya basu samu kammala aikin cikin lokaci ba.

Nan take kuma shugaban hukumar ya amince da kara musu makonnin, kuma ya umrci daraktan tantancewar daya tabbata ya magance musu matsalar da suke fuskanta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel