Shugaba Buhari zai koma bakin aiki yau – Inji Fadar shugaban ƙasa

Shugaba Buhari zai koma bakin aiki yau – Inji Fadar shugaban ƙasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana ma yan Najeriya shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kma bakin aiki a yau Litinin 13 ga watan Maris.

“Shugaba Buhari zai koma bakin aiki yau” – inji Fadar shugaban ƙasa

“Shugaba Buhari zai koma bakin aiki yau” – inji Fadar shugaban ƙasa

Babban hadimin shugaban kasa ta bangaren watsa labarai Garba Shehu ne ya bada wannan tabbaci a daren jiya, a wata hira da yayi da majiyar mu, inda yace yau shugaba Buhari zai mika ma majalisun dokokin kasar nan takardan shaida musu ya dawo, kuma zai fara aiki.

“Inshaa Allahu, yau a za’a aika ma majalisun dokoki wasikar, kuma inshaa Allahu, yau shugaban kasa zai koma bakin aiki.” inji Shehu.

KU KARANTA: Murnar dawowar Buhari: Wani ya yi rabon kilishi Naira 200,000 kyauta don murna

Da safiyar ranar Juma’a ne dai shugaba Buhari ya dawo daga kasar Birtaniya inda ya kwashe kwanaki 50 cif cif ana duba lafiyarsa, sai dai yayin da shugaba ke birnin Landan, ya mika ma mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ragamar tafiyar da mulki.

Amma a wata yar kwarya kwaryan walima da aka shirya ma shugaba Buhari bayan ya dawo, ya shaida ma mukarrabansa cewar dalilin dawowarsa na dawowa ranar juma’a itace don ya kara samun hutu a cikin ranakun karshen mako, sai ya koma aiki ranar Litinin.

Majiyar mu ta shaida mana tun bayan dawowar shugaba Buhari daya shiga sashinsa dake fadar shugaban kasa, bai fito ba, don ko a masallacin juma’a ba’a hangi keyarsa ba.

Shima kaakakin shugaban kasa Femi Adesina ya bayyana ta shafinsa na kafar sadarwar zamani Twitter @FemAdesina cewar shugaba Buhari zai aika ma majalisar dokoki wasikar da zata shaida musu ya dawo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel