Tashin Dala: CBN za ta cigaba da sakin daloli

Tashin Dala: CBN za ta cigaba da sakin daloli

Babban bankin CBN na kasa ya bayyana cewa za a cigaba da sakin dalolin Amurka domin a takawa tashin dalar burki.

Tashin Dala: CBN za ta cigaba da sakin daloli

Tashin Dala: CBN za ta cigaba da sakin daloli

Bankin CBN na kasa ya bayyana cewa za a cigaba da daukar matakai domin takawa Dala burki. Wani babban Jami’in bankin Ayo Teriba yace yana sa rai cewa yunkurin da Bankin na CBN ke yi zai kawo sauki a kasuwar canji.

Jami’in ya bayyana cewa Bankin na CBN ya gaza sakin daloli ne ga kasuwar saboda karancin farashin gangar mai da aka samu da kuma karancin yawan man da ake hakowa a kullum a baya. Wannan dai ya sa kudin kasar waje na Najeriyar yayi kasa sosai.

KU KARANTA: EFCC na binciken tsofaffin Gwamnoni

Yanzu haka dai Bankin na CBN na sakin dalolin Amurka a kan kari ga bankuna domin a sauko da farashin dalar wanda da tayi karanci a kasuwa. Babban Jami’in na CBN yace nan da wasu ‘yan lokacin darajar dalar za ta fadi.

Tsohon Gwamnan babban bankin CBN Farfesa Charles Soludo ya soki tsare-tsaren tattalin arziki na wannan Gwamnati. Soludo ya bayyana wannan ne a wani taro da aka yi domin gyara tattalin arzikin Najeriya. Soludo yace Jam'iyyar Buhari ta zo da maradu da alkawura iri-iri kafin ta hau mulki sai dai yanzu babu wani abin a zo- a gani a kasa Inji Farfesan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel