EFCC za ta binciki tsofaffin Gwamnoni

EFCC za ta binciki tsofaffin Gwamnoni

Hukumar EFCC za ta biyo ta kan tsofaffin Gwamnonin da ake zargi da laifin sata a kasar. Tuni ma dai har wani tsohon Gwamnan Zamfara ya sauya sheka zuwa APC a karshen wannan makon

EFCC za ta binciki tsofaffin Gwamnoni

EFCC za ta binciki tsofaffin Gwamnoni

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa tace za ta binciki tsofaffin Gwamnonin kasar da ake zargi da laifin sata a lokacin da su ka rike asusun Jihohin su. Wani babban Jami’in Hukumar Ishaq Salihu ya bayyana haka a karshen wannan makon.

Shugaban Hukumar na Yankin kudu-maso-kudu ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a Ranar Asabar. Jami’in yace ba shakka Hukumar EFCC za ta binciki tsofaffin Gwamnonin da suka maida asusun Jiha cikin aljihun su.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai yi kakkaba kwanan nan

EFCC za ta binciki tsofaffin Gwamnoni

EFCC za ta binciki tsofaffin Gwamnoni

Jami’in yace muddin Ibrahim Magu na rike da Hukumar EFCC babu wanda ya isa ya kawo masu wana cikas ko ya taka masa burki. Jami’in na EFCC yace yanzu fa babu wanda za a dagawa kafa a wannan bincike da. Hukumar ta yaba da kokarin Kotu da ta yankewa tsohon Gwamnan Adamawa daurin shekaru 5 a gidan yari.

Sai ga shi an buge da cacar baki tsakanin tsohon Gwamnan Edo Adams Oshiomole da kuma tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya Farafesa Charles Soludo. Oshiomole ya zargi Soludo da azurta wasu bankuna da sama da Biliyan 8 yayin da zai karya darajar Naira lokacin yana rike da CBN. Soludo dai ya karyata wannan zargi gaba daya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras
NAIJ.com
Mailfire view pixel