Buhari ya shirya koma wa aikin ranar Litinin, 13 ga watan Maris

Buhari ya shirya koma wa aikin ranar Litinin, 13 ga watan Maris

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai koma bakin aiki a ranar Litinin mai zuwa, 13 ga watan Maris

- Dawowar Buhari bakin aiki ya biyo mayan wani hutun kwanaki 51 da ya tafi na ganin likita wanda ya sanya yan Najeriya cikin damuwa

- Ana ta rade-radin cewa babu mamaki shugaban kasar ya bukaci Karin lokaci don ya huta amma an kore wannan rade-radin

Bayan hutun ganin likita na kwanaki 51 a birnin Landan, shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin komawa bakin aiki a gobe, 13 ga watan Maris.

Buhari ya shirya koma wa aikin ranar Litinin, 13 ga watan Maris

Buhari ya shirya koma wa aikin ranar Litinin, 13 ga watan Maris

A cewar jaridar The Guardian, wata majiya a fadar shugaban kasa ta kore rade-radin cewa shugaban kasa shugaban kasa ya kaddamar da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ya ci gaba da aiki na wasu makonni, cewa shugaban kasa Buhari ya yi kwari kamar ginshiki.

A lokacin da shugaban kasa Buhari ya dawo fadar Villa a ranar Juma’a ya bayyana cewa “Naji sauki sosai. Da gangan na dawo a kusa da karshen mako, don mataimakin shugaban kasa ya ci gaba sannan kuma ni na ci gaba da hutawa.

An canja wannan tsarin daga baya kusan yamma a ranar Juma’a 10 ga watan Maris, lokacin da majiyoyin shugaban kasa suka sanar da dawowar shugaban kasa bakin aiki a gobe. Wannan ya janyo sharhi da dama a tsakanin wasu yan Najeriya da ke kokwato idan shugaban kasar ya samu cikakken lafiya da zai fara gudanar da aikin da ya rataya a wuyan sa.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman a shafin zumunta da kafofin watsa labarai, Femi Adesina, a shafinsa na twitter a ranar Juma’a da ta gabata, ya ce shugaban kasa zai aika wasika ga majalisar dokoki don ya dawo bakin aiki, kamar yadda yayi daidai da kundin tsarin mulki.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel