Abubuwa 4 da zasu faru idan shugaba Buhari ya koma ofis gobe Litinin

Abubuwa 4 da zasu faru idan shugaba Buhari ya koma ofis gobe Litinin

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai koma bakin aiki ranan Litinin, 13 ga watan Maris bayan ya dawo jinya daga kasar Birtaniya.

Abubuwa 4 da zasu faru idan shugaba Buhari ya koma ofis gobe Litinin

Abubuwa 4 da zasu faru idan shugaba Buhari ya koma ofis gobe Litinin

Karanta abubuwa 4 da zasu faru idan Buhari ya koma aiki:

1. Buhari zai aika wasika zuwa majalisan dattawa

Game da cewar mai Magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, Buhari zai aika wasika ga majalisan dattawa akan cewa lallaifa ya dawo kuma zai cigaba da aiki.

2. Za’a cigaba da ziyarce-ziyarce

Ko shakka babu, shugaba Buhari zai karbi bakuncin mutane da yawa ranan Litinin duk da cewa ya fadawa kowa ya zauna a jiharsa ba zai sun zi Abuja ba.

3. Osinbajo ya mia masa ragamarsa

A ranan Juma’a da Buhari ya dawo, ya fadawa mataimakinsa cewa zai cigaba da zama mukaddashin shugaban kasa har zuwa karshen mako. Sannan ya dawo aiki ranan Litinin.

Saboda haka, Farfesa Osinbajo zai mikawa Buhari ragamar mulkin da ya dana yayinda Buhari ke jinya

4. Gamawa da kuma canje-canje

Kamar yadda aka sani, za’a cigaba da ganawa da ma’aikatan gwamnati. Ana sa ran Buhari zai gana da ministocinsa ranan Litinin sannan kuma an samu labarin cewa zai yi wasu canje-canje a gwamnatinsa.

Rahoton da jaridar Punch ta samu na nuna cewa canje-canjen da za’ayi zai shafi wasu kusoshi a fadar shugaban kasa

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel