Buhari na fama da cutan ‘Anaemiya’ – Farfesa Williams

Buhari na fama da cutan ‘Anaemiya’ – Farfesa Williams

- Farfesa Femi Williams yace bayanin da shugaban kasa yayi na cewa an kara masa jini na nuni da cewa yanada ‘Anemiya’

- Shugaba Buhari yace bai taba rashin lafiya mai tsawo irin wannan ba

Buhari na fama da cutan ‘Anaemiya’ – Farfesa Williams

Buhari na fama da cutan ‘Anaemiya’ – Farfesa Williams

Farfesa Femi Williams wanda sanannen likitan Anatomic Pathology na Landan da Ireland ya bayyana cewa shugaba Buhari na fama da Anemiya.

Shugaba Buhari dai ya dawo ne a ranan Juma’a, 10 ga watan Maris bayan jinayan kwanaki 51 a kasar Birtaniya.

KU KARANTA: Sojoji sun fitittiki yan Boko Haram a Sambisa

Farfesa Willaims yayi wanna bayani ne a wata hira da jaridar The Nation inda yace:

“Yanzu mun san abinda ke damun Buhari bisa ga gwajin da akayi kuma yana nuna cewa yana fama da Anemiya

“An wallafa sakamakon gwajinsa a ranan 26 ga watan Fabrairu, 2017 a jaridar The Nation inda ak fadi cewa an kara masa jinni.

“Amma sakamakon da aka samu daga baya ya nuna cewa ya samu sauki kuma ya daina cutan Anemiya.

“Samun karfinsa bayan Karin jinni da kuma dawowansa ya nuna cewa an samu nasara wajen warkar da Anemiyan.”

Ana sa ran dai ranan Litinin, Shugaba Muhammadu Buhari zai koma bakin aiki.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel