Sojojin Najeriya na cigaba da farautar ‘Yan Boko Haram

Sojojin Najeriya na cigaba da farautar ‘Yan Boko Haram

Rundunar Sojojin Najeriya suna cigaba da farautar ‘Yan ta’addan Boko Haram a Dajin Sambisa da ke Arewa-maso-Gabashin Kasar a halin yanzu haka.

Boko Haram: Sojoji na cigaba da luguden wuta a Sambisa

Sojoji na cigaba da luguden wuta a Sambisa Inji Birgediya Janar SK Usman

Kamar yadda mai magana da bakin Sojin Najeriya Birgediya-Janar SK Usman ya bayyana Sojojin Najeriya na ta cigaba da kwakulo ragowar ‘Yan Boko Haram da ke cikin Dajin Sambisa. Yanzu haka dai Rundunar Sojojin sun daga babu kama hannun yaro.

Rundunar Sojin kasar na Operation Lafiya dole sun kara kaimi wajen kakkabe ‘Yan Boko Haram da ke Yankin, Janar din yace ana cigaba da fatattako ‘Yan Boko Haram da ke makale a wasu kauyuka na Dajin Sambisa.

KU KARANTA: Rikici ya barke a Kasar Yarbawa

Sojojin Najeriya na cigaba da farautar ‘Yan Boko Haram

Sojojin Najeriya na cigaba da farautar ‘Yan Boko Haram

A wani hari da Rundunar Operation Lafiya dole na Bataliya ta 159 suka kai a Garuruwan Manlumudori da Filari da Itari da Mirimari da wasu Garuruwa sun yi nasarar kakkabe wasu ‘Yan Boko Haram da ke Yankin. Sojojin dai sun yi gaba inda suka cigaba da fatatttako ‘Yan ta’addan da ke mafaka a Yankin.

Tsohon Gwamnan Jihar Edo Kwamared Adams Oshiomole ya bayyana cewa idan har shugaba Buhari ya fito takara a zaben 2019 zai yi nasara babu wata tantama. Oshiomole ya bayyana irin kokarin da aka yi wajen kawo karshen rikicin Boko Haram wanda suka addabi Jama’a a da.

Sojojin Najeriya na cigaba da farautar ‘Yan Boko Haram

Sojojin Najeriya na cigaba da farautar ‘Yan Boko Haram

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan Boko Haram sun yi barna

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel