Oshiomole yace idan Buhari ya fito takara zai yi nasara

Oshiomole yace idan Buhari ya fito takara zai yi nasara

Tsohon Gwamnan Jihar Edo Kwamared Adams Oshiomole ya bayyana cewa idan har shugaba Buhari ya fito takara a zaben 2019 zai yi nasara babu wata tantama.

Oshiomole yace idan Buhari ya fito takara zai yi nasara

Oshiomole yace idan Buhari ya fito takara zai yi nasara

Tsohon Gwamna Adams Oshiomole ya bayyana abin da yasa Muhammadu Buhari zai lashe zabe mai zuwa idan har ya fito takara a 2019. Oshiomole yace ba za ka hada yadda Gwamnatin PDP ta bar mulki da kuma yanzu ba.

Adams Oshiomole ya bayyana irin kokarin da aka yi wajen kawo karshen rikicin Boko Haram. Tsohon Gwamnan yace da PDP ke mulki da yanzu ‘Yan Boko Haram sun gama keta Najeriya. Gwamnan ya kuma bayyana irin kokarin da aka yi na kawo karshen satar mai irin na lokacin shugaba Jonathan.

KU KARANTA: Fayose ya nemi a sa Buhari a addu'a

Oshiomole yace idan Buhari ya fito takara zai yi nasara

Oshiomole yace idan Buhari ya fito takara zai yi nasara

Oshiomole yace Gwamnatin Buhari tayi namijin kokari kawo yanzu inda yace idan kuma rashin lafiya ce ba yau aka fara samun maras lafiya a Duniya ba. Oshimole yace Buhari yayi abin da ya dace bayan da ya rubuta Majalisa takarda da zai tafi.

An yi ‘yar rigima da musayar kalamai tsakanin shi Adams Oshiomole da kuma Farfesa Charles Soludo tsohon Gwamnan CBN na kasa. Soludo ya zargi Gwamnatin Buhari da jagwalwala tattalin arzikin Najeriyda inda Oshiomole ya maida masa da martani yace yayi barna a CBN.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel