Buhari na bukatar addu’ar mu – Gwamna Fayose

Buhari na bukatar addu’ar mu – Gwamna Fayose

– Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose yayi magana game da rashin lafiyar Buhari

– Ayo Fayose yace shugaba Buhari na bukatar addu’o’in mu

– Gwamna Fayose yace shugaba Buhari na da aiki a gaban sa

Buhari na bukatar addu’ar mu – Gwamna Fayose

Buhari na bukatar addu’ar mu – Gwamna Fayose

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Peter Fayose ya kira ‘Yan Najeriya su cigaba da yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a domin ya samu sauki. Gwamnan yace akwai aiki na gyaran kasar a gaban shugaba Buhari.

Ayo Fayose yayi wannan magana ne kamar yadda muka samu labari a wajen ta’aziyyar tsohon Gwamnan Yamma Janar Adeyinka Adebayo a Birnin Ado-Ekiti. Fayose yace kowa ya damu game da rashin lafiyar shugaban kasar don haka a taya sa da addu’a.

KU KARANTA: Boko Haram: Sojojin Najeriya na cigaba da bambamin wuta

Buhari na bukatar addu’ar mu – Gwamna Fayose

Buhari na bukatar addu’ar mu – Gwamna Fayose

Fayose yayi addu’a Ubangiji ya ba shugaban kasar karfin tafiyar da mulkin yace domin yana bukatar gyara abubuwa da dama da suka tabarbare a kasar. Duk da haka dai Fayose yace za suyi ta addu’a Buhari ya sauko da farashin dala zuwa N200 sannan kuma samu saukin abinci.

Jam’iyyar PDP mai adawa tace dole a sanar da ‘Yan Najeriya cutar da ke damun shugaban kasa Muhammadu Buhari. Inda tace tana murna da dawowar shugaban.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel